Majalisar wakilai a Najeriya ta buƙaci hukumar sadarwa ta ƙasar NCC da ta tsawaita lokacin sake rijistar layukan waya zuwa makwanni goma.

Wannan ƙudiri ne da wani ɗan majalisa a jihar Delta ya miƙa kudirin ga majalisar a yau Laraba.

Majalisar ta ce ya kamata a duba buƙatu na ƴan Najeriya ganin yadda hidima bikin kirsimeti ke ƙaratowa.

Hukumar sadarwa a Najeriya NCC ce ta bada makwanni biyu don sake rijistar layukan kira na waya, tare da haɗashi da lambar katin dan ƙasa.

Sai dai majalisar ta buƙaci a tsawaita lokacin zuwa makwanni goma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: