Hukumar lura da tuƙi a jihar Kano Karota ta sanar da kama wata mota maƙare da giya da misalin karfe 2:30 na daren ranar Alhamis kuma kuɗinta ya kai naira miliyan 25 .

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabunusi Abubakar Ƙofar Na’isa ne ya sanar da haka ta cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai.
Haka kuma ya ce hukumar ta samu nasarar kama miyagun kwayoyi da kuma wasu kayan da wa’adinsu ya ƙare bayan hukumar ta samu rahoto.

Sanarwa ta rawaito cewa shugaban hukumar karota Baffa Babba Ɗan Agundi ya na cewa ƙofa a bude take ga mutane a bisa duk wani abu da suka gani ba su gamsu da shi ba.

Sannan ya ce a shirye hukumar take ta kai mamaya duk wani waje da ake haramtaccen kasuwanci a duk fadin jihar.
Daga ƙarshe kuma ya bayyana cewa an miƙa barasar da aka kama zuwa ga hukumar Hizbah don faɗaɗa bincike.