A ƙasa da kwanaki ashirin an samu nasararar kama ɓata gari 83 tare da wasu bindigogi a jihar Benue.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Muƙaddas Garba ne ya ce daga ranar 20 ga watan Disamban shekarar da ta gabata zuwa 5 ga watan Janairun da muke ciki suka sami nasarar hakan.
Waɗanda ake zargi akwai ƴan fashi da makam, masu garkuwa da mutane, ɓarayin ababen hawa da kuma ƴan ƙungiyar asiri.

Ya ce an sami nasarar kwato bindigu 13 daga hannun ɓata garin.

Kwamishinan ƴan sanda Muƙaddas Garba ya tabbatar da cewar ƴan sanda a jihar na aiki tuƙuru wajen ganin sun daƙile dukkan laifuka a jihar.
Sannan ya miƙa saƙon godiya ga mutanen jihar bisa haɗin kai da suke basu har suka cikka nasrarorin.