Tun a watan Satumban shekarar da ta gabata mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya yi shela don a tara masa kuɗin da zai yi sabuwar waƙa.

Kimanin watanni huɗu kenan har yanzu shiru babu batun wakar da ya bukaci talakawa su tura naira dubu dubu don yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sabuwar waƙa.
Ko da Mujallar Matashiya ta tuntuɓi Rarara a wancen lokaci, ya ce yana so ne ya nunawa duniya har yanzu Buhari yana da masoya.

Duk da cewa mawaƙin ya bayyana cewar ba da jimawa ba zai lalubo ayyukan shugaban ya bayyana cikin sabuwar waƙar, amma har yanzu babu labarin hakan.

Ko da yake ba iya shi kaɗai ya zo da wannan sabon salo ba, ba da jimawa ba mawaƙi kuma jarumi Adaam Zaango yaa yi shela cewar dukkan masoya Atiku Abubakar su tura masa kuɗi don ya yi masa waƙar kiranyi amma shi ma shiru kake ji wai mallam ya ci shirwa.
Mujallar Matashiya ta tuntuɓi Rarara a kan lambara wayarsa sai dai bai sami damar ɗagawa ba don jin ina aka kwana da zancen.
Tun a lokacin dai mutane daban-daban sukai ta tura kuɗaɗe kuma suna wallafawa a shafukan sada zumunta.