Wani rahoto da ke fitowa daga jihar Yobe a gabashin Najeriya na nuni da cewa mayaƙan Boko Haram sun hallaka sojoji shida a wani harim bam.

Harin ya biyo bayan sojoji sun hallaka mutane 26 da ake zargi mayakan ƙungiyar ne.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar bayan sojoji shida da suka mutu akwai wasu da suka jikkata.

Al’amarin ya fau a ranar Asabar ɗin da ta gabata a ƙauye Gonar Kai da ke ƙaramar hukumar Gujba a jihar.

Sai dai sojojin sun daƙile harin tre da kwato wasu makamai na Boko Haram kamar yadda mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin ya bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: