Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Za A Yi Zaɓe Kuma A Binciki Waɗanda Suka Yi Badaƙala A Kasuwar Kwari – Ganduje

Gwamna Jihar Kano Abdullahi Ganduje Ya Tabbatar Da Cewa Dole Sai An Yi Zabe A Kungiyar Kasuwar Kwari, Kuma Dole Sai An Samarwa Kasuwar Doka

  • Ya kuma tabbatar da cewa za a binciki wadanda su ka wawashe kudin tallafi da a ka ba kasuwar da masu karbar kudaden ‘yan China

Saboda gujewa ci gaba da lalacewa ta fuskar ƙungiyar ƴan kasuwa da kuma tsamo kasuwanci daga dulmiyewa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin cewa dole ne sai an yi zabe sahihi kuma sai an samar da Doka wacce za ta dinga tafiyar da harkar gudanarwa ga kasuwar Kantin Kwari a Kano.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne lokacin da wakilcin dandazon ‘yan kasuwar ya kai masa wata ziyarar ban girma da nuna goyon baya kan sababbin tsare tsare da gwamnatin Kano ke samarwa ga kasuwar. Sun kai wannan ziyara ne karkashin jagorancin Sharhabilu Ɗanlami Musa.

Ya karbe su ne lokacin ya na tsaka da taron Majalisar Zartaswa na Jiha tare da Mataimakinsa da Sakataren Gwamnati da Kwamishinoni da dukkan membobin majalisar Zartasawa ta jiha.

“Mun yi abubuwa da yawa a wannan kasuwa ta Kwari saboda mu na da kishin ganin ci gaban harkar kasuwanci a Kano. Mun yi tituna, mun yi ginin zamani ga ‘yan tebura, ga ofishin ‘yan sanda saboda tsaro, ga Masallaci da kuma ragowar abubuwan ci gaba da mu ka kawo a wannan kasuwa,” in ji Gwamnan.

Ya ci gaba da cewa, “Nan gaba kuma akwai shirin za mu sa katanga mai aminci sannan mu yi babbar Kofa shige da fice a wannan kasuwa. Bayan nan kuma za mu sa na’urori na zamani saboda kula da harkar tsaro.”

“Dokar da za a yi a kan wannan kasuwa, a halin yanzu, dokar ta na gaban Majalisar Dokoki ta Jiha, bayan sun gama nasu aikin ni kuma zan sa wa dokar hannu. Saboda haka dole ne sai mun yi wa wannan kasuwa doka. Dole ne kuma sai an yi zabe sahihi na kungiyar ‘yan kasuwa a wannan kasuwa ta Kwari,” ya kara tabbatarwa.

Ya kuma nuna cewar, Hukumar Karbar Korafi Da Hana Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano, ta kawo masa bayanin cewa sun karbi bayani daga wasu ‘yan kasuwar Kwari cewar an yi badakala ga kudaden tallafi da a ka karba da sunan kasuwar.

A kan hakan sai ya ce “Za a gudanar da bincike kan wannan ta’asa da su ka yi. Ba wanda zai yi abinda ya ga dama. Kuma a kyale shi a haka.”

Sannan gwamnan ya ce ya samu wani korafin na cewar wasu ‘yan kasuwar su na karbar kudaden ‘yan China ba bisa ka’ida ba. Ya ce “Shi ma wannan za a yi bincike a kai. Ba zai yiwu a bar mutane su yi ta abinda bai kamata ba sannan su na karyar cewar wai su ne ‘yan kasuwa ko shugabanni.”

Ya tabbatar da cewa “…duk wani shakiyi ko dan cuwa-cuwa karyarsa ta kare. Da Ikon Allah dole sai mun gyara tsare tsaren kasuwanninmu.”

Saboda kuma a kara kyautata harkar kasuwanci a wannan kasuwa ta Kwari, gwamna Ganduje ya ce “Za mu Gina muku asibiti wanda zai dinga ba ku magani kyauta, a samar da likitoci da za su dinga ganin marasa lafiya kyauta.”

Daga karshe kuma gwamnan ya yi kira gare su da su tabbatar su na amfani da shawarwarin ma’aikatan lafiya wajen kiyaye yaduwar cutar COVID-19 a harkokinsu na kasuwanci da kuma a gidajensu.

Shugaban tawagar Sharhabilu ya tabbatarwa da Gwamnan cewa “Ya Maigirma Gwamnan Kano mun zo wajen nan ne dan mu kara tabbatar maka da goyon bayanmu ga duk wasu tsare tsare da wannan gwamnatin ta ke son yi a wannan kasuwa ta mu ta Kantin Kwari.”

Ya kara da cewa a matsayinsu na halastattun ‘yan kasuwar Kwari su na maraba da ayyukan alheri da gwamnatin Gandujen ta yi a kasuwar.

Daga nan sai ya lissafa abubuwa kamar tituna, da kantinan da a ka yi wa ‘yan tebura da karamin ofishin ‘yan sanda da ofishin jami’an kashe gobara. Ya kara da cewar “Ya Maigirma Gwamna mun ga yadda ka mayar mana da wannan kasuwa daga tsohon yayi zuwa sabon yayi.”

Sai kuma ya rufe da korafin cewa an yi tsawon shekaru sama da goma sha shida ba a yin zabe a kungiyar ‘yan kasuwa ta Kantin Kwari.

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Laraba, 13 ha Watan Janairu, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: