Aƙalla sojoji biyar ne suka mutu yayin da sama da goma suka jikkata a sakamakon wani bam da ya tashi a wani yanki na Chibok da ke jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewar bam ɗin wanda ke binnewa a ƙasa ne kuma ya tashi a yayin da sojojin suke tafiya a mota.
Al’amarin ya faru a safiyar Alhamis ɗin da ta gabata a ƙauyen Yahi da ke ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno.
Babban jami’in sa kai a yankin Yohanna Bitrus ya bayyana cewar motocin sojojin sun lalace ciki har da ta babban kwamandan soji da ke kula da runduna ta 117 wanda tuni ya mutu.
Al’amarin hare-hare na ci gaba da faruwa a sassa daban daban na Najeriya a daidai lokacin d ake fuskantar rikicin mayaƙan Boko Haram a gabashin ƙasar, a wasu yankunan arewacin ƙasar kuwa ana fama da rikicin masu garkuwa da mutane da sauran ƴan bindiga.