Wata kotun majistire a Oredo da ke jihar Edo ta yanke hukunci a kan wasu mutane 17 da aka samu da aikata karya dokar da aka saka don kaucewa kamuwa da Korona.

Mutanen sun karya dokar kulle wadda gwamnatin jihar ta saka daga ƙarfe goma na dare zuwa biyar na safe.
An saka dokar don rage yaduwar cutar Korona a fadin jihar.

Waɗanda aka kama an sakasu aikace aikace a harabar kotu har tsawon awanni uku bisa laifin da suka aikata.

Mafi yawa daga cikin mutanen da aka kama an kama su ne a babban birnin garin Edo wato Benin.
Ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a jihar Edo, ko da a jiya Talata, sai da aka samu mutane 36 waɗanda suka kamu da cutar.