Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dokar ɗaurin watanni shida ga mutanen da suke ƙin saka takunkumi a Najeriya.

Shugaba Buhari ya saka hannu a kan dokar da za a hukunta masu bijirewa bin dokokin kaucewa kamuwa da cutar Korona a ƙasar.

Ciokin dokokin akwai ɗaurin watanni shida ga mutanen da bas a saka takunkumin rufe baki da hanci.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar wanda fadar shugaban ƙasa ta kafa Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja.

Ya ce an samar da dokar ne ganin yadda ake karya ƙa’idar da masana suka saka don kaucewa kamuwa da cutar.

Dokar za ta yi aiƙi ne ga mutanen da suka bijirewa saka takunkumi rufe baki da hanci, sai kin wanke hannu, da kuma ƙin bayar da tazara sai waɗanda suke ƙin shafa man kashe kwayoyin cutuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: