Rundunar ƴan sanda a jihar Taraba ta ce ƴan bindigan da suka sace mutane sun ƙetara zuwa wani daji a jihar Benue.

Matasan da aka sace su 26 an gudu da su zuwa wani daji da ke jihar Benue a jiya Juma’a.

Masu garkuwa da mutanen da suka sace matasan sun buƙaci a basu kuɗin fansa naira miliyan 52 kafin sakin matasan.

An yi garkuwa da matasan ne a ranar Larabar da ta gabata a kan titin wukari zuwa Takum na jihar.

Mai magan da yawun ƴan sanda a jihar Taraba David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin wanda yNa ce ƴan bindigan sun gudu da matasan zuwa wani daji da ke jihar Benue.

Guda cikin iyalan waɗanda aka sace sun bayyana cewar kowanne mutum za a biya kuɗin fansa nira miliyan biyu kafin sakinsa.

Ana ci gaba da samun ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane a jihohi daban-daban a Najeriya musamman Arewaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: