Rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi ta kama wani da yake yin safarar makamai ga ƴan binga.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan wanda ya ce sun kama wani babban mai garkuwa da mutane a jihar.

Ya ce a ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata, sun kama wani mai suna Ibrahim Bulun ɗauke da bindigogi ƙirar gida.

Wanda ake zargin ya amsa cewar yana safarar makamai ne ga ƴan bidigan.

DSP Nafi’u Abubakar ya ce suna ci gaba da bincike a kan waɗanda aka kama, kuma za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: