Rundunar ƴan sanda a jihar Delta ta gano wata gawa da masu garkuwa da mutane suka kashe sannan su ka binneta a cikin wani ƙaramin rami.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Muhammad Ali ne ya tabbatar da hakan ya ce sun samu rahoton sace matar ne yayin da ɗan ta ya kai bayanai a gare su.

Masu garkuwan sun kashe matar ne bayan sun karɓi kuɗin fansa naira dubu 650.

Sai dai rundunar ta yi nasarar kama guda daga cikin wanɗanda su ka yi garkuwa da matar.

Kwamishinan ya bayyana cewar, ɗaya daga cikin waɗanda suka sace matar suka kashe ta ne ya jagoranci tawagar ƴan sanda zuwa wajen da suka binneta.

Matar mai suna Philomena Ogadi mai shekaru 54 an kasheta sannan aka binne ta a wata gona kusa da babbar hanyar Benin zuwa Onitsha a ƙaramar hukumar Ika South ta jihar Delta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: