A yau Alhamis da misalin ƙarfe 2:49 gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi allurar rigakafin sa.

An yi wa gwamna Ganduje allurar ne a asibitin koyarwa na Murtala da ke kwaryar birnin Kano.
Yayin da yake jawabi, kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce a shirye suke don ganin sun gudanar da allurar rigakafin ga al’ummar jihar.

A jiya Laraba aka kawo rigakafin allurar ƙunshi 209,520 wanda ake sa ran za a yi wa kashi 70 na mutanen jihar Kano.

Babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya ce likitan gwamna ganduje na musamman dakta Yahaya Muhammad ne ya yi wa gwamnan rigakafin.
Tun a baya, gwamna Ganduje ya yi zama na musamman da kwamiti da shugabanni daban-daban ciki har da shugabannin tsaro da na lafiya a kan yadda za a gudanar da allurar rigkafin a jihar Kano.
