Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan ƙasar da su zama tsintsiya maɗauri guda.

Cikin saƙon taya murnar tunawa da haihuwa tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu, shugaba Buhari ya ce sam Najeriya ba za ta yi daɗi ba idan ya kasanace an samu rarrabuwar kai.

Shugaban ya bayyana cewar duk da kasancewar Najeriya ta ƙunshi mutane daban-daban waɗanda ke da harsuna da addini mabambanta amma zai fi daɗi idan ya kasance tana dunƙule a matsayin ƙasa guda ɗaya.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron taya murnan tsohon gwamna Legas Bola Ahmad Tinubu ne ta hanyar Internet daga fadar sa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Taron na bana an yi masa laƙabi da haɗin kanmu shi ne arziƙinmu, kuma shi ne karo na 12 da aka yi a tarihi

Leave a Reply

%d bloggers like this: