Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya buƙaci Fulani makiyaya da su ƙauracewa jihar a wannan lokaci.

Gwamna ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar zartarwa na jihar a yau Talata.
Gwamna y ace a wannan lokaci da jihar ke cikin ruɗani, sakamakon hare-haren da ake kai wa jami’an yan sanda.

David Umahi ya ce a halin yanzu ba Fulani makiyaya ne matsalar jihar ba, a cewar gwamnan makiyayan un bar jihar da kan su sannan ake samun hare-haren da ake ƙaddamar wa a kan jami’an ƴan sanda.

Kuma y ace ya buƙaci fulanin da su ƙauracewa jihar har sai an samu zaman lafiya a jihar.
Al’amarin korar makiyaya daga jihohin kudu ya janyo cece-kuce daga mutanen Najeriya, wanda ake ganin hakan ya saɓa da kundin tsarin mulki da ya bai wa ƴan ƙasar damar gudanar da rayuwarsu a duk inda su ke so na ƙasar.