A yau Asabar mayaƙan sun yi mummunan ta’adi a garin na Geidam kamar yadda mazauna garin su ka bayyana.

Mazauna garin sun ce ƴan Boko Haram ɗin sun ɓuya a garin ne kuma yayin da sojoji su ka tafi su ka fito a yau Asabar su ka yi ta’adi a garin.

Mayaƙan sun kwashi kayan abinci tare da ƙone gidaje a garin duka a yau Asabar.

Rahotanni sun ce an datse hanyoyin sadarwar wayoyi wato Network a garin, wanda ya sa ba a samun mutane a wayoyin su.

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari garin Gaidam a jihar Yobe tare da raba wasu takardu ga mutanen garin.

Mayaƙan sun shiga garin ne a yammacin jiya Juma’a da yamma kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta bayyana.

Sun shiga garin ne ta iyakar Najeriya da Nijar sannan su ka fara harbe-harbe al’amarin da ya sa mutanen su ka gudu cikin gidajen su.

Baya ga haka mayaƙan Boko Haram suna zubar da wata takarda a ƙasa wadda su ke neman amincewar mutanen garin domin kafa daular su a garin.

Wani ganau ya bayyana cewar mayaƙan sun shiga garin da ƙarfinsu ɗauke da makamai a hannun su.

Tuni aka aike da jiragen soji zuwa garin lamarin da ya sa mayaƙan su ka lafa, sai daiu ƴan sandan jihar Yobe sun tabbatar da cewar har yanzu mutanen na cikin garin bas u fit aba.

Sannan za su bayar da cikakken bayani bayan sun kammala tattaara bayanai a dangane da harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: