Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar lambar  shirin haɗa lambar ɗan ƙasa da layukan waya zai taimaka wjen magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da sabon tsarin samar da lambar ɗan ƙasa a fadarsa da ke Abuja.

A yayin ƙaddamarwar ministan sadarwa a Najeriya Dakta Isah Ali Pamtami ya gabatarwa da jami’an gwamnatin lambar ɗan ƙasa mai dauke da lambar NIN.

Shugaban y ace mallakar lambar ɗan ƙasa zai taimakawa ƴan ƙasar wajen samun aikin yi da sauransu tare da samar da tsaro a ƙasar.

Hukumar sadarwa a Najeriya ce ta samar da tsarin haɗa lambar ɗan ƙasa da layujan wayar salula a wani salo na taimawa tsaro a ƙasar.

An tsayar da ranar 30 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a rufe yin rijistar, sannan hukumar ta ce an  yiwa mutane sama da miliyan 50 lambar ɗan ƙasa wanda za a iya haɗa layukan waya kusan miliyan 200 a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: