Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gargaɗi masu kai hare-hare ga ƴan sanda da sauran jami’an tsaro a kudu maso gabashin ƙasar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar.

Sanarwar ta miƙa ta’aziyya da jaje ga waɗanda su ka rasa ƴan uwansu.

Hare-Haren da ake kai wa wanda ake zargin ƴan ungiyar IPOB mutanen nan da ke fafutukar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.

Sannan ya yi kira ga shugabannin gargajiya a yankin da su ja kunnen mutanen da kai kai hare-haren.

A makon da ya gabata ma sai da aka kashe ƴan sanda sama da 10 tare da ƙona motoci da sauran wurare a chaji ofis daban-daban na jihohin kudu maso gabashin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: