Ƙasar saudiyya ta amince da ske buɗe wuraren shan shisha bayan tsawon lokaci da aka ɗauka a kulle saboda cutar Korona.

An amince da buɗe wuraren shan shishan da suke a sarari sannan aka haramta sha a wuraren cin abinci.
Ma’aikatar kula da karkara da birane a ƙasar ce ta bayar da wannan dama kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar SPA ya rawaito.

Sai dai mutanen da aka yi wa rigakafin cutar Korona kaɗai aka amince a sayarwa da shisha.

Za a buɗe wuraren ne daga ranar Litinin kamar yadda sanarwar ta bayyana.
An rufe wuraren shan shisha da gahawa da kuma gidajen abincin ne saboda fargabar yaduwar cutar Korona.
A wannan lokaci ana ɗaukar mataki na sassauta dokar yayin da cutar ke raguwa a wasu wuraren.