Gwamnatin jihar Kano ta umarci iyaye su mayar da ƴaƴansu makarantun daga yau Lahadi.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Sanusi Ƙiru ne ya bayyana hakana a sanarwar dabkakakin hukumar Aliyu Yusuf ya bayyana.
Kwamishinan ya buƙaci iyaye su mayar da ƴaƴansu waɗanda suke makarantun kwana daga yau Lahadi, su kuwa masu zuwa makarantun jeka ka dawo su koma a gobe Litinin.

Gwamnatin Kano ce ta saka ranakun 16 da 17 ga watan da muke ciki domin komawar ɗaliban makaranta bayan taƙaitaccen hutun sallah da aka bayar.

Gwamnatin ta buƙaci iyaye daɗaliban da su mutunta wannan doka da ta tsara.