Wasu da ake zargi mayaƙan ƙungiyar IPOB ne masu rajin ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA sun kai hari wani chaji aofis ɗin yan sanda tare da kashe biyu daga ciki.

Bayan kashe jami’an biyu an ƙone chaiji ofis ɗin ƴan sandan duka a jihar Abia kudu maso gabashin Najeriya.

An kai harin ne a ofishin yan sanda na Apumiri Ubakala da ke ƙaramar hukumar Umuahia ta kudu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar kafin kai harin jami’an ƴan sana sun samu bayanan siriir a kan harin da aka kai.

Sannan an bada umarnin rufe ofishin ko ƙara ƙarfin jami’an tsaro sai dai ba a yi ko ɗaya daga ciki ba.

Kudu maso gabashin Najeriy`a na fuskantar hare-hare daga ƴan ƙungiyar IPOB wanda hakan ke ƙara sakwarkwatar da tsaro a Najeriya.

Ƴan ƙungiyar IPOB na kai mafi yawan hare-haren

Leave a Reply

%d bloggers like this: