Connect with us

Labarai

An Karrama Ganduje Da Naɗa Masa Alkyabbar Girmamawa Ƴar Asali

Published

on

 

Limami a Masallachin Haramayn na Birnin Makkah Mai Tsarki kuma shugaban Cibiyar Nazarin Larabci na Jami’ar Ummul Qura Farfesa Hassan Ibn AbdulHamid Al-Bukhari ya yabawa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa hidimtawa Musulunci da Gwamnan ke yi tare da gwamnatinsa.

Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya jagoranci tawagar wasu mashahuran malaman Jami’ar Ummul Qura, zuwa ga fadar gwamnatin Jihar Kano, yau Litinin, don sanar da Gwamnan abinda ya kawo su Jihar, bisa gayyatar Jami’ar Bayero ta Kano.

“Alhamdulillah tun mu na can mu na samun labaran aikhairin da gwamnatin ka ke yi wajen tallafawa cigaban Addinin Musulunci. Mun yi murna matuka da wannan labari da muke samu. Kuma mun zo mun gani ma da idonmu,” ya ce.

Ya kara yabawa yadda Gwamnan na Kano ya ke abubuwa saboda ci gaban al’ummarsa. Sa’annan nan ya tabbatar da cewa kullum a shirye su ke da su tallafawa Jihar ta Kano.

An bayyana cewar sun zo Kano ne bisa gayyatar jami’ar Bayero ta Kano, kan wata horaswa ta musamman da za su yi ga Alkalai da kuma daliban ilimi. Wannan ce kuma horaswa irin ta ta hudu da su ka yi a kasar nan.

A nasa jawabin Gwamna Ganduje ya bayyana yadda danganta ta jima tsakanin Jihar Kano da kasar Sa’udiyya tun shekaru da yawan gaske da su ka wuce.

Ya ce “…irin wannan dangantaka ce dadaddiya kuma mai inganci tsakaninmu, ta sa har Kasar ta Sa’udiyya ta bude wani ofishin jakadanci a nan Kano. Wanda duk wata alakarmu da wannan kasa mai Tsarki ta Sa’udiyya ta nan ne mu ke farawa.”

“Alhamdulillah mu na da wani shirin na musamman dama da kasar Sa’udiyya wanda mu ke tura Malamai a na yi musu bita ta sati biyu ko uku. Daga baya bayan nan mun tura mata guda 100 domin su ma su amfana da irin wannan horaswa. Matan kuma Malamai ne na makarantun Islamiyya,” in ji Gwamnan.

Nan gaba kuma za a kara tura mutane wajen irin wannan horaswa. Kamar yadda ya bayyanawa wadannan manyan baki.

Cikin farinciki da walwala ya yi bayanin yadda Gidauniyarsa ta Ganduje Foundation ta ke yin kokarin gaske wajen hidimtawa Musulunci.

Kamar yadda ya ce “Wannan Gidauniya ni ne da kai na nake daukar nauyin dun aikace aikacen da a ke yi. An musuluntar da mutane sama da Dubu Ashirin (20,000) wadanda ba su da addini ko daya, sun shiga cikin da’irar Musulunci, Alhamdulillah. Kuma sama da shekaru 30 nake tare da wannan gidauniyar tawa.”

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Litinin, 31 ga Watan Mayu, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Wani Ɗan Majalisa Ya Buƙaci A Rushe Majalisar Dattawan Najeriya

Published

on

Wani dan majalisa tarayyaa mai wakiltar Ovia a jihar Edo Denis idahosa ya bayyana cewa yakamata a soke majalisar dattawan kasar saboda irin asarar kudaden da gwmnatin ke yi akan su.

Denis ya bayyana haka cikin wata hira da aka yi da shi da kamfanin dillacin labarai na kasa Najeriya NAN.

Ya ce ya na fadin hakane ba don ya na daga cikin majalissar wakilai bane, a a ya yi nazarin yadda Najeriya ta karar da kudade ga majalissar dattawa kuma duba da yadda ake fama da rashin tattalin arziki a kasar.

ya ci gaba da cewa Najeriya na iya kirkirar majalisa ta baidaya wadda za ta dinga gabatar da duk abinda kasa ke bukata.

sannan majalissar wakilai kaso da yawa na aikin majalissa ita ce ta ke yi, yakamata a rushe ta datttawa a bar guda daya duk da cewa sau uku su ke zama a majalisa a duk sati sai a kara ya zaman za ai zaman sau biyar a mako.

ya ce ba dabara ba ce ace ya zamana suna da majalisu guda biyu a kasa gashi ana fama da rashin kayan aiki a matsayin su na yan kasa dole indai ana so a samu ci gaba a rushe majalissar dattawan Najeriya domin rage matsin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Iyalan Marigayi Goni Aisami Sun Koka A Kan Rashin Hukunta Sojojin Da Su Ka Kasheshi

Published

on

Iyalan shaharraren malamin adinin nan da aka yiwa kisan gilla wato Shiek goni Aisami dan asalin jihar Yobe sun bayyana cewa sun damu matuka akan yadda har yanzu ba su ji an hukunta sojan da ya hallaka mahaifin nasu ba.

Daya daga cikin iyalan malamin mai suna Abdullahi Goni Aisami ya bayyana cewa ba su ga dalilin da zai haifar da tsaiko a cikin lamarin ba.

ya ce sun shiga fargaba da tashin hankali saboda kin samun wata hujja akan kin gurfanar da sojin a gaban kotu.

ya ci gaba da cewa suna cikin matsalar musamman daga bangaren matan malamin da su ke gani kamar ba wani hukunci akai ba.

Sai dai a bangaren hukuma kakakin rundunar yan sandan jihar Yobe DSP Dungus ya bayyana cewa tun lokacin da su ka kammala bincike suka turawa hukumar shariar domin gurfanar da wadannan sojoji guda biyu a gaban kotu.

Sannan ya ce an yi nasarar yin hakan a ranar 19 ga wata Satumba aka zauna domin sauraren shari’ar.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ASUU Kan Watsi Da Umarnin Kotu

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen Kungiyar Malaman Jami’a akan ƙin bin dokar Kotun Ma’aikatun Kasa ta Najeriya na komawa bakin aikinta daga dogon yajin aikin da ta ke yi.

Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka, ya ce Kungiyar tana faɗawa ‘yan Najeriya zancen da babu sui akan batun cikashe fom din daukaka karar akan umarnin kotu.

Ministan ya yi kira ga kungiyar akan ta mutunta umarnin kotun, ta kuma koma kan aikinta yayin da su ke kokarin ganin sun sasanta akan sauran matsalolin.

Ministan ya yi wannan batun ne ta wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi wadda Olajide Oshundun, mataimakin darektan yaɗa labaran ministan ya sanyawa hannu.

A cewar sa kungiyar ba ta fadin asalin gaskiyar yadda aka yi da ita ga mutanen ƙasa da kuma mambobinta, dangane da batun daukaka kara bisa umarnin da kotu ta yi mata ranar 2 ga watan Satumba.

Sai dai ASUU ta bukaci a ba ta damar daukaka kara. Sannan ta hada wannan bukatar tata da kuma takardar daukaka karar da ta ke da niyar yi da zarar an bata wannan damar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: