Aƙalla mutane 30 ne su ka mutu a sanadin wani hatsarin jirgin ƙasa da su ka yi karo da juna a Pakistan.

Hatsarin ya faru a kudancin Pakistan wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane 30 yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Wasu daga cikin mutane sama da 50 da su ka ji munanan raunnuka tuni aka garzaya da su asibiti domin basu agajin gaggawa.

Wani jami’I a ɓangaren gwamnati ya bayyana cewar tarago takwas sun lalace lamarin da ya sa ake wahala don ceto fasinjan da su ka maƙale.

Jiragen biyu a su ka yi karo da juna sun tintsira wanda hakan ya sa wasu da dam aba a ceto su a kan lokaci ba.
Gwamnatin ƙasar ta ce jiragen biyu na Milat ne sai jirgin Sir Syed.