
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin kammala titin nan da ya taho daga Jakara zuwa Gorondutse ba da jimawa ba.
Har ma a nan take ya ba da umarni ga Kwamishinan Ayyuka da ya yi gaggawar bin takardun aikin, dan ganin a ina a ka kwana kuma a ina za a tashi.

Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke kaddamar da Makon Shirin Tsaftace Birnin Kano, wanda a ka kaddamar a katafariyar kwatar nan ta Jakara, wacce ta zarce har zuwa Kwakwaci, gaban Gidan Jarida na Triumph, yau Talata.

Titin wanda tsohuwar gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta fara kuma ta watsar ya dade ya na ci wa mutanen yankin tuwo a kwarya.
Daidai lokacin da Gwamna Ganduje ya yi wannan maganar kammala aikin titin sai wajen ya dau wata irin sowa daga daruruwan mutanen da su ka je wajen waccan kaddamarwa.
Ya ce “Mun biyo ta wannan titi mai muhimmanci mun ga yadda aikinsa ya kasance. Yanzu haka ina tare da Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, na kuma ba shi umarnin da ya koma ofis ya dauko fayil din a ga yadda aikin yake, saboda a yi gaggawar kammala aikin.”
“Wannan titi mai muhimmanci, na Sheikh Mahmud Salga, da ya faro daga kan titin Malam Aminu Kano, Gorondutse, zuwa Jakara bola, za mu tabbatar an kammala shi ba da jimawa ba,” in ji shi.
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Talata, 22 ga Watan Yuni, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com