Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake ƙara wa’adin rufe layukan wayar da ba a haɗa su da lambar ɗan ƙasa ba.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar sadarwa a Najeriya hadi da hukumar yi waƴan ƙasa shaida su ka fitar, sun ce sun yi haka ne da nufin bai wa ƴan ƙasar damar hada layukan wayarsu.

Hukumar ta ƙara wa’din zuwaranar 26 ga watan Yuli mai kamawa.

Bayan ike da buƙatar hakan, gwamnatin tarayya ta duba buƙatar tare da amincewa da ƙara wa’adin.

Hukumomin sun ce sun samar da wadatattun hanyyin gudanar da mallakar katin ɗan ƙasa, kuma da shi ne z a iya haɗa layukan wayar da ake amfani da su wajen kira.

An fitar da sanarwar ne a yau Talata wadda ke ɗauke da sa hannun wakilai daga hukumomin biyu.

A halin yanzu an yi wa mutane sama da miliyan 57 rijistar ɗan ƙasa, sannan kowacce rijista akwai damar hada ta da layukan waya uku zuwa huɗu.

Hukumar yi wa ɗan ƙasa rijista ta fitar da sanarwar cewar a cikin mutane sama da miliyan 200 a Najeriya mutane miliyan 57.3 ne su ka mallaki lambar ɗan ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: