Gwanatin jihar Sokoto ta yi wa furzuna 32 afuwa tare da sakin su don gudanar da rayuwar su.

Babban jojin jiha kuma kwamisinan shari’a a jihar Sokoto Sulaiman Usman ne ya bayyana haka a madadin gwamnan jihar.
Ya ce an yi wa mutane 32 afuwa ne tare da hada su da yan uwansu domin ci gaban jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Babban jojin jihar y ace gwamnatin jihar ta wanke wadanda aka saka daga laifukan da ake zargi sun aikata.

Kuma yana fata sakin nasu zai amfanar da al’umma wajen samun ci gaba da wadata a tsakanin al’umma.
Waɗanda gwamnatin ta yi wa afuwar sun sha alwashin kaucewa duk wata hanya da za ya sa su kuma aikata wani laifi a nan gaba.