Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da tsige shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Barsita Muhuyi Magaji rimin Gado.

A zaman majalisar na yau Litinin, biyo bayan wata takardar ƙorafi da ofishin babban akawu na jihar ya gabatarwa majalisar.
Wasiƙar ta ci gaba da cewar shugaban hukumar ya ƙi amincewa da sanya wani matsayin akawun hukumar.

Tun a makon da ya gabata ake ta yaɗa labara zargin cire shugaban hukumar wanda ake zargin batun na da alaƙa da gwamnan Kano.

Zargin da ake yi a kan hakan ya samo asali biyo bayan wani ƙorafi da aka gabatar masa wanda ake zargin wani ɓangare na iyalan gwamna da hannu a ciki.
Tsawon wata guda kenan da faruwar lamarin, wanda ake zargin hakan ce ta sa gwamnan ya nemi majalisar dokokin jihar da ta tsige shugaban a matakin da yake.