Hukumar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta ja hankalin mutane a kan wasu shafukan sadarwa da ake budewa da sunan shugaban asibitin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun mahukunta a asibitin Hauwa Muhammad Abdullaho ta fitar, ta ce sam shafin ba da masaniyar shugaban aka bude ba.

Ana amfani da wani shari da aka buɗe da sunan shugaban asibitin Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe wajen shelanta tallan aiki ga mutane sannan a nemi wasu kudade daga gare su da wanda tace sam ba su da alaka da hakan.

Hukumar ta nesanta kanta da wannan shafin tare da duk wata kafa da ake amfani da sunan nemawa mutane aiki da sunan asibitin.

Haka kuma sun ja hankalin mutane da su kula tare da watsi da duk wata sanarwar neman aiki tare da neman kuɗi kafin su samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: