Fadar sarkin musulmi a Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar lll ta sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji aa ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ganin wata ya fitar a jiya.
An ga watan Zulhajji lamarin da ya sa yau Lahadi ya zamto ɗaya ga watan Zulhajji.

Sanarwar ta taya musulmin kasar murnar shiga wannan wata mai albarka.

Wata ne da musulmi ke gabatar da ibadar aikin hajji.
Ibada ce da ke cikin rukunan musulunci.
Kuma watan Zulhajji wata ne na 12 cikin jerin watannin kalandar musulunci.