Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wata ganawa da wakilai a zauren majalisar dattawan Najeriya a daren yau Talata.

A cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar Ahmad Lawal ya karanta a yau yayin zaman majalisar.

Shugaba Buhari zai gana da mambobin majalisar su 109 don tattaunawa a kan batun da ya shafi al’amuran tsaron ƙasar.

Wasiƙar gayyatar na ƙunshe da bayanin ranar da za a yi taron da kuma lokaci da wurin da za a yi.

Za a yi taron ne a yau Talata da misaim ƙarfe 8 na dare zuwa abin da ya sawwaƙa a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Hakan ya biyo bayan ci gaba da kai munanan hare-hare da yan bindiga su ka ci gaba da yi tare da yaɗuwar ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Ganawar za ta mayar da hankali ne a kan al’amuran da su ka shafi tsaron a Najeriya.

A na sa ran wasu daga cikin masu ruw da tsaki a ɓangaren tsaro za su halarci ganawar a yau.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: