Masarautar Kano ta soke hawan babbar sallah a bana.

An soke bikin hawan sallar ne don bin shawarar gwamnatin tarayya a kan soke bikin don hana yaduwar cutar Korona

Madakin Kano Alhaji Yusif Nabahani ne ya bayyana hakan yau Litinin.

Ya ce sarkin Kano ALhaji Aminu Ado Bayero ya umrce shi da ya sanar da soke bikin hawan salla a bana saboda fargabar yaɗuwar cutar Korona.

Hakan ya biyo bayan kiran da gwamnatin tarayya ta yin a soke hawan salla saboda fargabar yaduwar cutar Korona.

Daga cikin jihohin da aka buƙaci su janye bikin salla a bana akwai jihar Kano, sai Jihar Legas, da jihar Kaduna ,Plateau, sai jihar oyo, da Rivers.

Bikin hawan salla al’ada ce da ake yi sau biyu a duk shekara, yayin bikin ƙaramar sallah da kuma babbar sallar, sai wasu jihohin da ke ƙara wa a watan mauludi wanda su ke yin sallar Gani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: