Hukumar lura da tuƙi a jihar Kano KAROTA ta yi gargaɗi ga mutanen da ke shirin yin gudun wuce sa’a da ganganci yayin bikin sallar.

Kakakin hukumar Nabilisi Abubakar Ƙofar-na’isa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce an ware jami’ai sama da 1,500 domin hana cunkoso a titunan jihar Kano.

Sanna n hukumar ta gargadi masu shirin bai wa mutanen da  sheratun su bai kai na tuƙi ba, da su kiyaye hakan don faɗawa komar hukumar.

Hukumar ta ce za ta saka ƙafar wando ɗaya da duk wanda ta samu da karya dokar tuki a jihar.

Haka kuma hukumar KAROTA za ta kama duk wanda ya karya dokar tuki tare da gurfanar da shi a gaban kotu don girbar abin da ya shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: