Kwamishinan ilimi a jihar Kaduna ya ce ɗaliban da su ƴan bindiga su ka sace daga baya su ka kubuta za su rubuta jarrabawar NECO.

Dakta Shehu Muhammad ya bayyana haka ne yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

Ya ce ɗalibai 32 daga cikin 121 da ƴan bindiga su ka sace za su rubuta jarrabawar da a halin yanke ake kan yin ta.

A cewar kwamishinan iya ɗaliban da su ke ajin ƙarshe na kammala sakandire kuma su ka yir ijistar ne za su rubuta jarrabawar.

Ma’aikatar ilimi a Kaduna da hukumar shirya jarrabawar NECO za su tabbatar ɗaliban sun rubuta jarrabawar.

A Jiya Litinin wasu daga cikin ɗaliban da yan bindiga su ka sace su ka kuɓuta daga hannun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: