Aƙalla ƴan bindiga biyu a ka hallaka yayin da su ka je neman kuɗin fansa a jihar Taraba.

Tun da farko yan bindigan sun buƙaci a basu kudin fansa yayin da su ka sace wani dattijo a garin Sabon Gida a jihar.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Gassol ta jihar bayan sun sace wani tsoho mai suna Alhaji Gambo.

Jami’an sa kai na Bijilanti ne su ka yi nasarar kashe yan bindigan biyu yayin da su ka zo domin karbar kudin fansa.

Haka kuma jami’an sa kai sun yi ƙoƙarin kuɓutar da dattijon da ƴan bindigan su ka yi garkuwa da shi.

Al’amarin ya faru ne a garin Sabon Gida da ke ƙaramar hukumar Gassol ta jihar.

Sai dai rahotanni na nuni da cewar yan bindigan sun sha halaka mutanen gharin da wasu waɗanda ke makwaftaka da garin.

Najeriya na fuskantar rikicin ƴan bindiga musamman a wannan lokaci da lamarin ke ƙaruwa a jihohin rewacin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: