Rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin Operation Haɗin Kai ta sake karɓar tubabbun mayaƙan Boko Haram 18 a jihar Borno.

A wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce mayaƙan da ƴaƴan su 19.
Tubabbun ƴan Boko Haram ɗin sun kai kan su ne a ranar Laraba 4 ga watan Agustan da muke ciki.

Mayaƙan da iyalansu na zaune a ƙauyen Chingori, da wasu da ke cikin wasu ƙauyuka a cikin dajin Sambisa.

Mayaƙan sun miƙa makamansu da su ka haɗar da bindigu ƙirar AK47 da harsashai da sauran makamai.
Rundunar ta ce mayaƙan sun miƙa mata wasu kuɗi naira dubu bakwai da ɗari bakwai.
Sanarwar ta ce ƙasa da makwanni biyu, mayaƙan Boko Hraam sama da 100 ne su ka tuba tare da kai kan su ga jami’an soji.
Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Faruƙ Yahaya ya jinjinawa jami’an nasa wajen samar da hadin kai da kuma nasarar da su ke kawo wa a arewa maso gabashin Najeriya.