Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da kammala wa mutane 195,591 rijistar katin zaɓen su baki ɗaya.

A sanarwa da hukumar ke fitarwa a kowanne mako, hukumar ta ce ta mutanen sun kammala bayar da dukkanin bayanan su ciki har da ɗaukar hotunan yatsun su da fuskar su.

Hukumar ta ce mutane 1,984,711 a ka karɓi bayanan su a kafar intanet.

Sanarwar wadda kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kai a kan katin zaɓe Festus Okoye ya sanya wa hannu.

Ya ce an tattara bayanan ne a yau Litinin ta misalin ƙarfe bakwai na safe.

Jihar Bayelsa ke da mafi rinjaye na adadin mutane 134,759 waɗanda su ka yi rijistar.

Sannan kaso mafi yawa na waɗanda su ka yi rijsitar a Najeriya jinsin maza ne wanda ke da mutane 1,119,675.

Hukumar ta fara yin rijsitar katin zaɓen a ofisoshin hukumar na ƙananan hukumomin Najeriya da helkwatar hukumomin a dukkanin jihohi a ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: