Wasu daga cikin manyan kwamandojin mayaƙan Boko Haram sun nemi afuwar yan Najeriya.

Kwamandojin da su ka miƙa wuya tare da ajiye makaman su, sun nemi afuwar yan kasar a bisa yadda su ka saka ta cikin wani hali.
Daga cikin kwamandojin da su ka nemi afuwar akwai babban kwamandan da ke koyar da yadda ake haɗa bama-bamai domin kai hare-hare.

Mai Magana da yawun rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne sanar da haka wanda ya ce mayaƙan sun miƙa kan su ne ga dakarun Operation Haɗin Kai.

Manyan kwamandojin sun miƙa kan su ne su da matan su da yayan su.
Mayaƙan sun nemi afuwar ƴan Najeriya ne yayin da babban soji mai lura da runduna ta bakwai ya ziyarce su a jihar Borno.
Jimillar mayakan da su ka mika wuya su 335, sai mata da ƴaƴan su su 746.
a wannan karon ne a ka fi samun yawan mayakan Boko Haram da su ka miƙa wuya ga jami’an tsaron Najeriya