Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba ta da wani zaɓi na ƙarshe illa sake saka dokar kulle don hana yaduwar sabuwar cutar Korona.

Ministan lafiya a Najeriya Dakta Osagie Ehanire ne ya sanar da haka yayin da ya ke bayani a gaban kwamitin yaƙi da cutar Korona wanda fadar shugaban ƙasa ta kafa a Abuja.

Ministan ya ce cutar Korona nau’in Delta na ci gaba da yaɗuwa sannan babu wata hanyar daƙile yaduwar ta illa sake saka dokar hana fita.

Sai dai y ace dokar hana fitar za ta yi aiki ne a wuraren da cutar ta fi ƙamari ba kamar yadda a ka saka a bay aba.

Sannan ya ce gwamnatin ƙasar na yin duk mai yuwuwa don ganin an bayar da rigakafin cutar gay an ƙasar kuma kyauta.

A wani mataki na sake samar da hanyar hana kamuwa da cutar, gwamnatin ƙasar ta biya wasu kudade don sake kawo rigakafin cutar wadda za a yi way an ƙasar.

Haka kuma akwai rigakafi da gwamnatin ƙasar ta karɓa wanda aka bayar don tallafa wa ƙasashe masu rauni ƙarƙashin tsarin COVAX.

Leave a Reply

%d bloggers like this: