Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe jami’an ta biyu yayin da ƴan bindiga su kai kutsa kai cikin makarantar horas da sojoji a Kaduna.

Mai Magana da yawun kwalejin ya tabbatar da kashe jami’an biyu a wata sanarwa da ya fitar a yau Taata.

Ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne a daren jiya Litinin wayewar Talata sannan su ka kashe mutane jami’an su biyu.

A na zargin ƴan bindigan sun sace sojoji guda biyu masu muƙamin Manjo, sai dai wani ya shaida wa BBC cewar an sace jami’in ne guda daya sannan a ka kashe biyu daga ciki.

Mai Magana da yawun makarantar Manjo BaSHIR Muhammad Jajira y ace ƴan bindigan sun kai harin ne ɓangaren gidaje a makarantn sannan sun tafi da jami’in su guda ɗaya.

Sanarwar ta ce dukkanin sauran mutanen da ke makarantar NDA a Kaduna na cikin ƙoshin lafiya.

Wannan dais hi ne harin da ke nuna maƙura wajen taɓarɓarewa tsaro a Arewacin Najeriya tun bayan da ƴan bindiga su ka tasamma kai hare-hare a ƴan kwanakin nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: