Hukumar lura da ingancin abinci a Najeriya NAFDAC ta ce za ta fara tantance masu tallan maganin gargajiya a jihar Kaduna.

Wani shugaba a hukumar Nasir Mato  ne ya bayyana haka a yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Kaduna.

Ya ce yawaitar masu siyar da maganin a jihar ne ya ja hankalin su don ganin sun tabbatar da tantance abin da al’umma ke ci ko sha a matsayin maganain gargajiya.

Hukumar za ta dauki wannan mataki ne don ganin an san adadin mutanen da ke siyar da shi da masu shigar da shi jihar don tabbatar da ingancin sa.

Kuma za su samar da takardar shaidar izinin siyar da magunguna da kuma bayan an yi wa mutanen da su ka cancanta rijist.

Hukumar ta ja hankalin masu siyar da maganin gargajiya a jihar da su tabbatar sun bi dukkan tsarin da a ka samar don tsaftace sana’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: