Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar halaka ƴan Boko Haranm Shida a wata musayar wuta da su ka yi tsakanin su.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar a Najeriya Onyema Nwachukwu ya fitar, y ace jami’an su sun yi nasarar kashe mayakan ne a ranar Labara.
A yayin musayar wutar rundunar ta yi nasarar kwato wasu bindigu ƙirar AK47 daga hannun ƴan Boko Haram tare da harsashi mai yawa.

Al’amarin ya faru ne a wani yanki tsakanin Damboa-bulabulin zuwa Maiduguri.

Haka kuma rundunar ta kwato wata mota daga ƴan Boko Haram sannan wasu kayayyaki daga ciki akwai kayan abinci da maganin sauro da kekunan hawa.
Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Fariuƙ Yahaya ya jinjina wa jami’an nasa a bisa nasarar da su ka samu na kashe mayaƙan.