Hukumar lura da tuki a jihar Kano sun kama mota ɗauje da tabar wiwi a jihar.

Hukumar ta kama motar ƙirar Golf a unwaguwar Ɗangwauro a jihar.

Kakakin hukumar Nabilisi Abubakar ne ya sanar da haka a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai.

Jami’an sun kama motar ranar laraba sannan shugaban ya mika ta ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Kano.

Shugaaban hukumar Karota Baffa Babba ya ce jami’an su na da kware wa ta musamman wajen kama miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: