Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce nan ba da jima w aba za ta ɗage takunkumin da ta saka wa kamfanin Tuwita a ƙasar.

Ministan yaɗa labarai da al;adu a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da haka bayan zaman majalisar zartarwa da ya gudana a Abuja.

Ministan ya tabbatar da cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da su ke tsakanin ɓangaren gwamnatin da kuma ɓangaren kamfanin na tuwita.

Lai Mohammed ya ce nan da kwanaki kadan za a ɗage takunkumin da aka ƙaƙaba wa kamfanin.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rufe kamfanin a ƙasar tare da umartar al’umar  ƙasar da su ƙarace wa shafin.

Hakan ya biyo bayan zargin da gwamnatin ƙasar ta yi wa kamfanin na bayar da dama ga wasu wanda ya haifar da rarravbuwar kai da kuma kunno fitina.

Sama da kwanaki 100 kenan da saka takunkumin da aka ƙaƙaba wa kamfanin a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: