Connect with us

Labarai

Yara Miliyan Guda Na Iya Ƙauracewa Makarantu A Najeriya – UNICEF

Published

on

Hukumar kula da ƙananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce a Najeriya an yi garkuwa da ɗalibai dama da dubu ɗaya.

A wani rahoto da hukumar ta tattara a kan yadda ƴan ta’adda ke kai hare-hare makarantu tare da sace ɗalibai.

Hukumar ta ce akwia yuwuwar fargabar sace ɗaliban ya yi sanadiyyar raba yara miliyan ɗaya daga makarantu.

Daga cikin makarantun da hukumar ta tattara alkaluman tare da fitar da hasashen akwia makarantun firamare da sakandire da kuma ɗaliban jami’a.

Hukumar ta ce fargabar rashin tsaro ce za ta yi silar raba mutanen daga makarantn.

Akwai ɗalibai da dama da ke hannun yan bindiga waɗanda aka sace daga makarantu daban-daban na jihohin ƙasar musamman ma arewaci.

Satar ɗalibai tare da neman kuɗin fansa wani saloo ne da yan bindigan su ka ɗauka daga baya, bayan ɗauki ɗaiɗai da su ke yi wa mutane a cikin gari ko kan tituna.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Iyayen Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jami’ar Tarayya Da ke Gusau Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Published

on

Iyayen dalibai matan da aka yi garkuwa da su a jami’ar tarayya da ke garin Gusau da ke Jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin Jihar.

Iyayen sun yi zanga-zangar ne domin neman a gaggauta sako musu ‘ya’yansu da masu garkuwa suka yi garkuwa dasu a cikin Jami’ar.

Masu zanga-zangar sun kuma nemi da gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare da sauran hukumomin tsaron Jihar da su yi duk mai yuwuwa wajen ganin an kubtar da ‘ya’yannasu cikin koshin lafiya.

Kazalika sun ce ‘yan bindigar sun neme wasu daga cikin iyayen daliban kan cewa ba za su sako daliban ba harsai sun tattàuna da gwamnatin Jihar.

Inda suka nemi da gwamnatin ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin an ceto ragowar wadanda ke hannun batagarin.

Masu garkuwar, sun yi garkuwa da daliban ne tun a ranar 22 ga watan Shekarar da mu ke ciki inda suka yi garkuwa da dalibai Mata 24 da wasu ma’aikata 10 a cikin Jami’ar, a lokacin da suka kai hari garin sabon Gida garin da dakunan kwana daliban suke.

Amma bayan garkuwa da daliban jami’an tsaro sun kubtar da dalibai 13 daga cikinsu Leburori Biyu, yayin da ragowar ke hannun maharan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Bayar Da Umarnin Yin Bincike Kan Harin Bom Ɗin Da Ya Kashe Masu Taron Maulidi A Kaduna

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan hallaka mutane da dama da jirgin yakin sojin Najeriya ya yi a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, tare da mika sakon jaje ga al’ummar Jihar.

Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar daukar matakin kaucewa kara faruwar hakan.

Gwamnan ya kuma bai’wa al’ummar Jihar tabbacin cewa za a tabbatar da tsaro, da bai’wa mutanen Jihar Kariya a lokacin da ake kokarin kawar da ‘yan ta’adda da sauran batagari a Jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko, domin ba su kulawar gaggawa da kuma daukar nauyinsu.

Jirgin ya hallaka mutanen a ranar Lahadi, a lokacin da suke tsaka da gudanar da bikin Mauludin a karamar Igabi ta Jihar bayan sanya musu bom da jirgin yayi har sau biyu.

 

 

Continue Reading

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Harin Sojojin Da Ya Kashe Mutane A Kaduna

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan mutanen da jirgin yakin sojin sama ya hallaka a Jihar Kaduna a lokacin da suke gudanar da taron mauludi a yankin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta Jihar.

Shugaban ya bayar da umarnin ne a safiyar yau Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar.

Tinubu ya nuna alhininsa akan lamarin tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar da ‘yan uwa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce shugaban ya bayar da umarnin a gudanar da bincike da kuma bai’wa wadanda suka jikkata kulawa ta musamman.

Tinubu ya kuma bukaci da mutane su bai’wa jami’an tsaron hadin kai wajen gudanar da bincike.

Sannan Tinubu yayi addu’ar neman gafara da rahmar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: