Gwamnan Zamfara Muhammad Bello Matawalle ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da BBC.

Gwamna Matawalle ya ce a halin yanzu ƴan bindiga na cin ɗanyar kubuwa saboda yunwa sannan su na yi wa mutanen da su ka sace bulala a maimakon ba su kudin fansa.
Gwamnan ya ce ƴan bindigan na yin haka ne sanadin toshe hanyoyin sadarwa na layukan waya da kuma rufe kasuwanni wanda hakan ya sa yunwa ke damun su.

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya ce babu ranar buɗe layukna sadarwar wayar salula a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin zantawar sa da BBC wanda y ace ana ci gaba da samun nasara da yaƙar yan ta’adda wanda hakan en ya sa aka rufe layukan sadarwa a jihar.
Gwamna Matawalle y ace a halin yanzu bay a sha’awar yin sulhu da yan bindigan da su ka addabi jihar tun da sun sha karya alƙawura da aka ƙulla tsakanin su a baya.
Gwamnan ya bayyana cewar ya na tattauna wa da takwarorin sa gwamnoni waɗanda ke makwaftaka da Zamfara don ganin sun ɗauki wannan mataki na katse layukan sadarwa a jihohin su.
Gwamna Matawalle ya ce a halin yanzu ƴan bindiga na cin ɗanyar kubuwa saboda yunwa sannan su na yi wa mutanen da su ka sace bulala a maimakon ba su kudin fansa.
Gwamnan ya ce ƴan bindigan na yin haka ne sanadin toshe hanyoyin sadarwa na layukan waya da kuma rufe kasuwanni wanda hakan ya sa yunwa ke damun su.
Gwamnatin Zamfara ta ɗauki matakin toshe layukan sadarwa na wayar salukla a jihar ne a wani salo na kawo ƙarshen ƴan bidnigan da su ka daɗe su na aikata ta’addanci a jihar.