Rundunar sojin Najeriya ta samar da wasu runduna guda uku wadanda za su dinga yaki da dukkanin ta’addanci a Najeriya.

An samar da rundunar Goledn Down, da Stil Water da kuma rundunar Enduring Peace kuma za a ƙaddamar da su a jihar Enugu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu, ya ce babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Farouƙ Yahaya ne zai ƙaddamar da rundunar.

Manufar samar da rundunar shi ne samar da zaman lafiya tare da daƙile ayyukan ta’addanci a ƙasar baki ɗaya.

Kakakin ya buƙaci al;umar garin kada su firgita da ganin jami’an sojin da kuma kayan aikin su, dukka shirye-shirye ne na ƙaddamar da dakarun rundunar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: