Gwamnatin jihar Neja ta ce za ta tabbatar ta kama dukkanin maus kai wa ƴan bindiga bayanai tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim ne ya sanar da haka a yayin taron yini guda don tattaunawa a kan yan bindiga wanda cibiyar tarihi da adana bayanai ta shirya a jihar.
An shirya taron ne domin tattauna batun yan bindiga waɗanda su ka addabi jihar.

Tuni gwmanatin ta kaffa kwamiti da zai dinga bin diddigin a kan shirin ƴan bindiga da su ka addabiw asu yankunan jihar.

Gwamnatin na buƙatar yaƙar jahilci, rashin aikin yi da talauci wanda hakan ke ƙara rura wutar rikicin ƴan bindiga.
An shirya taron ne a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai a jihar.
A na zargin ƴan bindiga da mayaƙan Boko Haram da kai hare-hare a jihar Neja wadda ta daɗe ta na fuskantar rikicn tsawon lokaci.