Hukumar kare fararen hula a Najeriya reshen jihar Kwara ta kama wani Garuba Ashin da ake zargi da satar dabbobi a jihar.

An kama Garuba a yayin da ya yi yunƙurin satar akuyoyin maƙocinsa mai suna Hassan Abubakar a yankin Iwala na jihar.

Tun tuni mutanen yankin ke zargin mutumin da satar dabbobinsu kuma hukumar ta kama shi a lokacin da yaƙe ƙoƙarin satar wasu.

Mai magana da yawun hukumar Babawale Afolabi ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen makon da ya gabata ya ce an jima ana satar dabbobi a yankin kuma mutanen sun yi zargin wanda aka kama da sace musu dabbobin.

Ya ƙara da cewar bincikensu ya gano cewar wanda aka kama ba shi kaɗai bane su na da yawa kuma za su ci gaba da bibiya domin kama ragowar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: