Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya buƙaci rundunar soji ta sake salon yaƙi da ƴan bindiga a jihar sa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Faruƙ Yahaya ya kai masa ziyara a fadarsa da ke gidan gwamnati.
Gwamna Tambuwal ya ce harion da yan bidniga su ka kai a kwanan nan ya kyautu ya sa rundunar sojin ta sauya salo wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Ya ƙara da cewa yana da kyau sauran jami’an tsaro da al’ummar gari su shigo domin bayar da gudunmawa yadda za a magance matsalar da ake fusknata ta tsaro a jihar.

Sannan ya ƙarfafi al’ummar jihar don ganin sun bayar da rahoto tare da nuna ƙin goyon bayan duk wani wanda ke taimaka wa yan bindiga.
Babban hafsan sojin ƙasan Farouƙ Yahaya ya yaba da irin ƙoƙarin gwamnan jihar tare da tabbatar da cewar rundunar sojin za ta ƙara ƙaimi don ganin an kawar da dukkan ƴan bindiga a jihar.
Kuma za su ci gaba da aiki da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar abin da su ka sa a gaba.