Babbar jam’iyyar APC mi mulki a Najeriya ta kafa kwamiti wanda zai bibiyi ƙorafe-korafe da ake yi a kan zaɓen shugabancin jam’iyyar na jihar Kano.

Kwamitin da babbar jam’iyyar ta aika jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dakta Tony.
Sakataren kwamitin Dakta Aminu Waziri ya bayyana cewar kwamitin zai fara sauraron ƙorafe-ƙorafen da ake yi a kan zaɓen da ya gubata.

Sannan kwamitin ya ayyana zaɓen da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a matsayin wanda zai karɓa.

Dakta Aminu Waziri ya bayyana cewar babbar jam’iyyar ta ƙaddamar da kwamitin ne domin yin sasanci da kuma sulhunta ɓangarorin da aka samu sabani a kai.
Haka kuma kwamitin zai kammala tattara bayanan sa a ranar Litinin tare da tantance sahihancin shugaban da kuma zaɓen da za ta karɓa.
A makon da ya gabata ne dai aka gabatar da zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a matakin jiha, kuma a jihar Kano aka samu ɓangare biyu da ke iƙirarin shugabancin jam’iyyar.